Sabon Maigarin Lakwaja yayi alkawarin zaman lafiya, hadin kai, cigaban Masarautar

Daga Musa Tanimu Nasidi

Sabon Maigari na Lakwaja a jihar Kogi, Mai Martaba Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi 1V, ya yi alkawarin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban masarautar a wani yunkuri na bunkasa ci gaban masarautar da ma jihar baki daya.

Kabir, wanda a kwanakin baya ne Gwamna Yahaya Bello ya amince da nadinsa a matsayin sabon Maigari na Lakwaja, ya yabawa gwamnan tare da yin alkawarin tabbatar da amincewar da aka yi masa.

Sarkin ya bayyana haka ne a fadar sa bayan an nada shi rawani a matsayin Maigari na bakwai na Lakwaja, wanda sarakunan karkashin jagorancin Talban Lakwaja, Rtd Air Marshall Ndatsu umaru, wanda babban limamin Lakwaja, Sheikh Muhammadu Aminu Sha’aban ya halarta a ranar Laraba, ya yi alkawari ci gaba da kyawawan abubuwan magabata.

See also  GM NIWA, An Binne Darda'u Cikin Hawaye

Ya ci gaba da cewa, za a ba da fifiko ga hadin kai da ci gaban al’ummarsa.

Mai Martaba sarkin ya bukaci al’ummar Masarautar da su hada kai da shi domin sauke nauyin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na Maigari da kuma sa gaba domin tunkarar kalubalen gaba.

Kabir Maikarfi ya kara godewa sarakunan da suka bashi mukamin Maigari. “Ina godiya ga duk wadanda suka dauki nauyin nadin nawa, sarakuna, masu mulki da kuma Gwamna saboda tabbatar da amincewa da nadin na.”

Sarkin ya kara da cewa al’ummar karamar hukumar Lakwaja da suka fito domin taya shi murnar nuna soyayyar da suke yi masa ya ta’azzara masa bayan da mai girma gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Adoza Bello ya tabbatar da shi.

See also  Troops clear notorious terrorists’ camp, recover materials for explosives

Ya kuma godewa daukacin iyalan gidan sarautar bisa goyon bayan da suke ba shi, ya kara da cewa “lokaci ya yi da za mu hada kai domin samar da zaman lafiya da hadin kai da ci gaban al’ummarmu.

Bukin rawani ya samu halartar Talban Lakwaja kuma tsohon gwamnan soja na jihar Kano, (Rtd)Air Marshall Ndatsu umaru, Dan Darma na Lakwaja, Barr Ahmed Nasir, Tafidan Lakwaja, Olu na Oworo, Rogan na eggan da sauran sarakunan gargajiya.

Gidan sarsutanMaigari da Musa Maigari,da duban jama’a ne sun kayi wa sabon Maigari Lakwaja mubaya’a

Visited 4 times, 1 visit(s) today
Share Now