Dimbin Jama’a A Yayin Da Maigari Lakwaja Ya Halarci Sallar Juma’ar Farko

Daga Musa Tanimu Nasidi

An samu dimbin jama’a a Lakwaja a ranar Juma’a yayin da sabon Maigarin Lakwaja, Alhaji Ibrahim Muhammadu Kabir Maikarfi 1V, ya halarci sallar Juma’arsa ta farko tun bayan hawansa karagar mulki a ranar Laraba.

Sarkin ya bar gidansa da ke unguwan Sarki, Lakwaja da misalin karfe 1:30 na rana a cikin murna da magoya bayansa da masu gadin fadar da masu rike da sarauta da sauran masu hannu da shuni suka raka shi zuwa masallacin.

Wakilinmu ya lura da cewa akwai jami’an tsaro sosai a kewayen gidan maigari da fadar da kuma masallacin inda matasa da dama suka yi dafifi domin hango sarkin.

See also  President -Elect Tinubu,Arrives Nigeria today,Says Onanuga

Shugaban riko na karamar hukumar Lakwaja, Hon Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC, Hon Maikudi Bature, Shatima na Lakwaja, Alhaji Muhammad Mabo Kasim, Maiyaki na Lakwaja, Alhaji Ali Lawal, Garguwan Lakwaja, Barr. Katu Sule, Hakimai da sauran ‘yan majalisar gargajiya na daga cikin manyan baki da suka halarci sallar Juma’a tare da Kabir.

A cikin hudubarsa babban limamin masallacin Juma’a na Lakwaja, Sheikh Muhammadu Aminu Sha’aban, ya yi kira da a bada hadin kai ga sabon Maigari, inda ya ce mutane da yawa za su iya neman mukami amma Allah ne kadai ke ba da shugabanci ga wanda ya so.

Al’uman garin Lakwaja sun nuna godiya ga Allah da ya basu zaman lafiya a masarautar, kuma sun bukaci sabon Maigari da ya yi adalci ga kowa.

See also  Kogi Assembly Speaker Receives Ward ‘E’ APC Leaders

Wakilin mu ya ruwaito cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne sarakunan masarautar Lokoja suka yi wa Alhaji Ibrahim Muhammadu Kabir Maikarfi 1V, rawani a wani gagarumin biki bayan Gwamna Yahaya Bello ya nada shi a matsayin Maigari na na bakwai a Lakwaja.

Visited 8 times, 1 visit(s) today
Share Now