
Daga Musa Tanimu Nasidi
Da Takarar Gwauna a karka shin Jamâiyyar All Progressives Congress, APC, Ahmed Usman Ododo, ya tabbatarwa sarakunan gargajiya, shugabannin kabilu da magoya bayan APC daga karamar hukumar Lokoja cewa zai yi nasara a zaben ranar Asabar.
Ya kuma yi alkawarin cewa tare da hadin gwiwar za su gina Lokoja da jihar Kogi a kan tsarin sabunta fata.
Ododo ya bayyana haka ne a wani taron tattaunawa da sarakunan gargajiya, âyan majalisar dokoki, shugabannin jamâiyya da masu ruwa da tsaki a fadin karamar hukumar Lokoja a wani bangare na taronsa na karamar hukumar sa gabanin zaben ranar Asabar.
Da yake godiya ga masu ruwa da tsaki na jamâiyyarsa da mambobin jamâiyyarsa bisa goyon bayan da suka nuna masa, Ododo ya bukace su da su yi alfahari da nasarar da Gwamna Yahaya Bello ya samu a Lokoja da kuma nasarar da ke jiran su.
âDole na mika godiya ta musamman ga kowane shugaban siyasa, dan jamâiyya da sarakunan gargajiya, a dukkan sassan wannan karamar hukuma.
Tare za mu ci wannan zabe. Tare za mu gina jihar Lokoja da Kogi.â Inji shi.