Dan Takarar Gwamnan Jihar Kogi A Jam’iyyar APC, Ododo Ya Gudanar Da Taron Majalisar Gari, Ya Ce “Wannan Wa’adin Na Mu Ne”.

Daga Wakilin Mu

Dan takarar gwamnan jihar Kogi a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Alhaji Ahmed Usman Ododo, ya ce ya tsara dabarun samar da ribar dimokuradiyya ga al’ummar karamar hukumar Lokoja idan aka zabe shi ranar Asabar.

Mai fatan gwamnan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da al’ummar karamar hukumar Lokoja, sarakunan kabilu, masu ruwa da tsaki, sarakunan gargajiya da shugabannin jam’iyyar APC na yankin.

Ododo ya ce bayan da ya gudanar da bincike mai zurfi, ya gano cewa dukkanin masu ruwa da tsaki na Lakwaja ba tare da la’akari da kabila, addini da siyasa ba suna da hadin kai.

See also  Barr. Ahmed Ya Taya Ganduje Murnar Nadashi A Matsayin Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa

Ya kara da cewa zaben da APC za ta zo ranar 11 ga watan Nuwamba, zabe ne na tabbatar da nasarorin da gwamna Yahaya Bello ya samu, musamman ci gaban ababen more rayuwa a Lakwaja.

Ya kuma yi kira ga iyaye da kada su bari ‘yan siyasa su rika amfani da ‘ya’yansu a matsayin ‘yan daba
“Ina so in yi kira gare ku dattawan mu, ku taimake mu mu aiwatar da aikin.”

Ya kuma ba su tabbacin jajircewar sa na ganin an samar da shugabanci na gari

“Ina so na tabbatar muku ba zan ba ku kunya ba, mu zo mu yi hidima da tsoron Allah, kasancewar mulki na Allah ne.” Inji shi.

See also  Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kogi (KOSIEC) ta yi alƙawarin gudanar da zaɓen gaskiya, mai sahihanci da karɓuwa.

Tun da farko, kakakin majalisar dokokin jihar Kogi, Rt. Hon. Yusuf Aliyu Umar ya jaddada kudirin karamar hukumar Lakwaja na kai Ododo ga nasara ranar Asabar mai zuwa.

Dan majalisar ya ci gaba da cewa Ododo zai karfafa kan nasarorin da gwamna Yahaya Bello ya samu.
“A karon farko tun bayan kafuwar dimokuradiyya a shekarar 1999, mutanen Lakwaja sun kasan ce tsintsiya kuma a shirye suke su yi magana da murya daya.

“Tabbas mutanenmu za su fito ranar Asabar mai zuwa domin kada kuri’unsu ga jam’iyyar APC da kuma dan takararta, Alhaji Ahmed Usman Ododo,” inji shi.

Taron ya samu halartar mamba mai wakiltar Lokoja, Kogi Federal Constituency, Hon. Suleiman Danladi Aguye, kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Hon. Muhammed Deedat Ozigi, Tijjani Bin-Ebiya Shehu,mamba Mai wakilita Lakwaja ta daya,Hon Mabo Kasim da Alhaji Sulaiman Babadoko.

See also  Dan Darman Lakwaja Barista Ahmed,Ya Taya Gov Ododo Murnar Nasarar Kotun Daukaka Kara

Sauran sun hada da: Shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Lokoja, Hon Maikudi Bature, kwamishinan harkokin mata, Hajiya Fatiha Buba.

Ba a bar sarakunan gargajiya, sarakunan kabilu, kungiyoyin mata da matasa ba.

Manyan batutuwan taron sun hada da, sakonnin fatan alheri daga sarakunan gargajiya, kungiyoyi, shugabannin jam’iyya da masu ruwa da tsaki a fadin karamar hukumar.

Visited 2 times, 1 visit(s) today
Share Now