
Daga Aliyu Musa Nasidi
A yayin da ake kara karatowa a zaben gwamna na ranar sha daya ga watan Nuwamba, 2023, a ranar Asabar din na ne daruruwan mambobin jam’iyyar PDP daga ward D a karamar hukumar Lakwaja suka sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Wadanda suka sauya sheka da suka hada da, Alhaji Umma Babadoko, tsohon sakataren kudi na karamar hukumar,
Hon Zakari Yaro (Akweka), PDP ward D Mai BA da shara’a,Jibrin Datti,Murtala Nasidi Tsohon shugaban matasa na PDP da umar Musa Tanko.
Shaura so hada da ;Muhammed Awwal,Lawal Barau,Tanimu Uba da Gambo Mohammed.
Da yake karbar sabbin mambobin, shugaban jam’iyyar APC, Hon. Maikudi Bature ya ce abin farin ciki ne na tarbar wadanda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC ta APC.
“Na yi matukar farin ciki ba don ina maraba da ku ku koma jam’iyyar ba amma don babu wata al’umma da ta dace ba tare da nagartattun shugabanni da masu kyakkyawar niyya ba.
“Wannan ne lokacin da jihar Kogi da yankinmu musamman za su samu shugabancin da ya dace ta wajin Mai rike da tutar jam’iyyar APC, Alhaji Usman Ododo, yana da idon basira kuma abin da muke bukata ke nan a jihar Kogi.”
“A cikin maraba da ku dole ne in ce kun yanke shawara mai kyau ta hanyar shiga jirgin kasa mai nasara da ci gaba.”
Tun da farko a nasa jawabin, shugaban tawagar, Alhaji Umma Babadoko, ya bayyana sauya shekar a matsayin matakin da ya dace.
Ya ce: “Mun fahimci cewa lokaci ya yi da za mu dauki matakin da ya dace mu shiga kungiyar da ta yi nasara.
Babadoko wanda ya bayyana komawar sa jam’iyyar a matsayin kokarin hada karfi da karfe da shuwagabannin mu wajen ganin cewa dan takarar jam’iyyar APC Ododo ya yi nasara a zaben gwamna a ranar 11 ga watan Nuwamba.
Ya kuma yi kira ga shugabannin jam’iyyar da su tafiyar da gwamnatin da ta hada da kowa da kowa a karshen zabe.
A nasa jawabin, mataimakin shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Lakwaja, Hon.Emmanuel Lonis ya tabbatar wa masu sauya shekar adalci a jam’iyyar.
“Na gode da kuka ga ya zama dole a koma cikin ‘yan uwa masu son ci gaba da kuma kasancewa cikin shirin raya jihar Kogi, kun dauki matakin da ya dace domin jam’iyyar ku ce kuma jam’iyyar da ta dace da ta bayar da gudumawa wajen ci gaban jihar” in ji shi.





