Dag Aliyu Musa Nasidi
Gabanin zaben gwamnan jihar kogi a ranar 11 ga watan Nuwamba, majalisar malamai ta jihar Kogi a ranar Lahadi a Lakwaja, ta bukaci jihar Kogi ta yi addu’ar samun nasara a zaben gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba.
Majalisar ta yi wannan kiran ne bayan kammala addu’o’in da ta gudanar a masallacin kugiyar da ke Lakwaja, tare da Sakatarenta, Alhaji Baba’ango Idris, ya ce halin da al’amura ke ciki a jihar, musamman zabe mai zuwa na bukatar sa hannun Allah.
“Mun taru a yau ne domin neman yardar Allah akan zabe mai zuwa, mu yi addu’ar samun zabe cikin lumana da nasara. Adu’o’i wadda Majalisar Malamai ta Jihar Kogi ta shirya, wani bangare ne na addu’o’in da ake ci gaba da yi, kuma za a ci gaba da gudanar da addu’o’i a manyan masallatai na tsakiya a fadin jihar a duk tsawon lokacin zaben,” in ji Baba’ango.
Ya kuma bukaci ’yan siyasa da su bi doka, su guji furta kalaman da za su iya kawo cikas ga al’amuran jihar da kuma dakile harkokin zabe.
“Muna kuma kira ga masu zabe da su kara hakuri da shugabanninsu a kowane mataki.
Majalisar ta yi addu’a ga Mai Martaba, Ohinoyi na Ebira land, Dr. Ado Ibrahim wanda ya rasu a safiyar Lahadi.