Daga Aliyu Abdulwahid
A yayin da ake Shirin zaben gwamnan jihar Kogi da za a yi ranar 11 ga Nuwamba, 2023, kungiyar sufurin babura ta Najeriya reshen jihar Kogi, ta amince da dan takarar jamâiyyar All Progressives Congress (APC) Alhaji Ahmed Usman Ododo da abokin takararsa, Comrade Salifu Oyibo Joel.
Shugaban NMTU na jihar, Kwamared Gimba Ibrahim ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Lakwaja ranar Laraba.
Shugaban ya ce, masu sufurin babura a jihar a karkashin jagorancinsa sun amince da yin aiki tare da hada kai domin samun nasarar Ododo a zabe mai zuwa.
âSaboda haka, ina kira ga duk mahaya okada da su fito su kada kuriâa ga APC a ranar 11 ga Nuwamba 2023,â in ji shi.
A cewarsa, kungiyar sufurin ta fito da kudurin nasu baki daya, wanda ya ce ya samo asali ne daga irin nasarorin da gwamna Yahaya ya samu, musamman a fannin tsaro da samar da ababen more rayuwa.
Kwamared Ibrahim ya bayyana kwarin guiwar cewa zaben Ododo zai jawo karin ayyukan raya kasa ga alâummar Oworo, mazaba Lakwaja ta Biyu da ma jihar baki daya.
Shi ya sa, âMuna da kwarin guiwa, alfahari da tsayawa tsayin daka tare da Alhaji Ahmed Usman Ododo, dan takararmu na jamâiyyar APC,â in ji shi.