Yarima Kabir Maikarfi Yayi Nasiha Akan Dokokin Allah

Daga Aliyu Abdulwahid

An bukaci al’ummar musulmi da su sadaukar da kansu ga dokokin Allah

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala Sallar Juma’a da aka gudanar a Sabon Masallacin Marigayi Abubakar Ola da ke Lokoja, Yarima Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi ya yabawa Alhaji Zakari Abubakar Ola da ‘yan uwansa kan gina masallacin a wani bangare na addu’ar Fidau na shekaru 10 na marigayi Abubakar Ola.

Ya bayyana marigayin a matsayin uba, wanda har yanzu soyayyarsa ga Lakwaja da ita mutane ba ta misaltuwa.

Maikarfi ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su nisanci duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiyar al’umma da ‘yan uwantakar ‘yan Adam.

Visited 4 times, 1 visit(s) today
Share Now
See also  Marigayi Abubakar Ola Masjid; Mun cika Burin Ubanmu.” - Zakari