Daga Abubakar Musa Nasidi
Shugaban gidauniyar marigayi Abubakar Ola (AOF)Alhaji Zakari Abubakar Ola, ya bayyana ginawa da kaddamar da masallacin Marigayi Abubakar Ola da ke cikin garin Lokoja a matsayin “cika buri da nufin mahaifinmu.” Marigayi Alhaji Abubakar Ola.
Zakari, ya bayyana hakan ne yau a Lakwaja a wajen kaddamar da sabon masallacin Marigayi Abubakar Ola da aka gina domin tunawa da shekaru 10 na addu’ar Fidau ga Alhaji Abubakar Ola.
Shugaban taro kuma memba mai wakiltar mazabar Lakwaja/Kogi, Hon. Suleiman Danladi Aguye ya yabawa Alhaji Zakari Abubakar Ola bisa hangen nesa da jajircewarsu ga addinin musulunci ta hanyar gina masallaci, wanda zai zama sadakatu’ jariya ga mahaifinsu da daukacin iyalansu.
Ya yi nuni da cewa masallacin zai kasance cibiyar hadin kai da zaman lafiya a tsakanin al’ummar musulmi.
Babban Limamin Masallacin Abubakar Ola, Ustaz Yakubu Shehu a cikin hudubarsa ya hori Musulmi da su sadaukar da lokacinsu wajen bautar Allah ta hanyar neman gafararSa da kuma ci gaba da yi wa iyayensu da suka rasu addu’a.
Imam Shehu ya yi kira ga musulmi da su yi koyi da Alhaji Zakari Abubakar Ola, wanda ya bayyana a matsayin mai taimakon al’umma.
Manyan abubuwan da aka gabatar addu’ar a cikin shekaru 10 na fidau sun haɗa da: rarraba kayan abinci, kayan masaku da bada magungu na ga marasa lafiya.
Sallar juma’a ta samu halartar Hon Shehu Tijjani Bin-Ebiya, memba mai wakiltar mazabar Lokoja 1, babban limamin masallacin juma’a na Markaz, ustaz Ibrahim Nyass Yusuf Abdullah tare da dubban musulmi.