Daga Musa Aliyu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da dakatar da shi daga ofishin Mista AbdulRasheed Bawa, CON, a matsayinsa na shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC domin ba da damar gudanar da bincike mai inganci a kan yadda ya aikata a lokacin da yake kan karagar mulki.
Hakan ya biyo bayan zarge-zargen cin zarafi da aka yi masa.
An umurci Bawa da ya gaggauta mika al’amuran ofishinsa ga Daraktan Ayyuka a Hukumar, wanda zai kula da harkokin ofishin Shugaban Hukumar har sai an kammala bincike.
Visited 4 times, 1 visit(s) today