
Gwamnatin Kano ta musanta yunkurin rusa sabbin masarautu
Gwamnatin jihar Kano ta ce har yanzu ba ta dau mataki kan sabbin masarautu guda biyar da tsohuwar gwamnatin Dr Umar Ganduje ta kafa. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan jihar Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Alhamis a Kano. Ya nuna cewa gwamnati ba ta tunkari majalisar dokokin…