Daga Musa Tanimu Nasidi
Sabon dan majalisa mai wakiltar mazabar Lokoja 1, Hon. Tijjani Shehu Bin-Ebiya, ya sha alwashin kawo sauyi ta hanyar wakilcin mazabarsa mai inganci a Majalisar.
Bin-Ebiya, wanda aka zabe shi a jam’iyyar APC a zaben majalisar dokokin jihar da ya gabata a mazabar Lokoja ta 1, ya ce mutanensa ba za su yi nadamar zabe shi ba.
Dan majalisar ya yi wannan alkawarin ne a Lokoja yayin wata liyafar tarba da al’ummar mazabar sa suka shirya domin tunawa da shi a ranar Talata.
Shehu ya tabbatar wa al’ummar mazabar Lokoja 1 da su inganta rayuwarsu ta hanyar karfafawa da kuma kyautata hulda da jama’a a matakin farko.
“Zan sadaukar da lokaci mai yawa na magance matsalolin al’umma da ke damun mazauna mazabar Lokoja 1, ba tare da la’akari da addini ko siyasa ba”. yace.
Ya yi godiya ga al’ummar mazabar Lokoja 1 da suka ba su wakilcin su a zauren majalisar inda ya jaddada cewa zai gabatar da kudirin doka da zai yi tasiri kai tsaye ga al’umma musamman matasa da mata da marasa galihu.
Tun da farko babban bako kuma babban limamin masallacin kutepa Imam Abu Bilal ya gabatar da lacca mai taken ” nauyi na shugabanci a Musulunci”.
Malaman addinin Musulunci sun shawarci shugabanni da su yi taka-tsan-tsan da nauyin da ke kansu a kan al’ummarsu, inda suka nakalto daga Alkur’ani mai girma cewa: “Hakika Allah yana yin umarni da ku mayar da amana ga wanda ya cancanta; Kuma idan kun yi hukunci a tsakãnin mutãne sai ku yi hukunci da ãdalci. To, madalla da abin da Yake azurta ku da shi. Lalle ne, Allah Yã kasance Mai ji, Mai gani.” 4:58
Ya ce mutum mai hankali wanda ya fahimci bukatun shugabanci ba zai yi kwadayin shugabanci ba, yana mai cewa al’umma ba za ta iya rayuwa ba tare da shugaba ba duk da nauyi kamar yadda ya zo a cikin Alkur’ani da Hadisi.
Ya bayyana shugabanci a matsayin wani babban nauyi a duniya da kuma lahira.
“Kowane ɗayanmu makiyayi ne kuma mai kula da garken tumakinsa ne. Hasali ma shugaban kasa yana da alhakin daukacin ‘yan kasar wanda ko shakka babu Allah zai tambaye shi yadda ya cika amanar da aka ba shi”. Yace.
Ya kuma taya dan majalisar murnar nadinsa a matsayin dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Lokoja 1.
Taron wanda ya gudana a harabar gidan ‘yan majalisar Karaworo, ya samu halartan babban limamin Lokoja Sheikh Muhammadu Aminu Sha’aban, wanda ya samu wakilcin Khalifa Arif Yabagi, Ustaz mansur Nayashi, Imam Abu’ Bilal.
Sauran sun hada da: Shugabannin APC, PDP, kungiyoyin mata, sarakunan gargajiya da sauransu.