Gwamnatin Kano ta kori Babban Sakataren Hukumar Alhazai

Daga Wakilin mu

Kasa da sa’o’i 24 da hawan kujerar shugabancin jihar Kano, da sanyin safiyar Talatar nan ne Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kori Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar, Muhammad Abba Danbatta.

Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature, wanda ya tabbatar da hakan a safiyar ranar Talata ta wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, ya kuma bayyana cewa gwamna Yusuf ya amince da nadin Alhaji Laminu Rabiu a matsayin sabon sakataren zartarwa na hukumar alhazai ta jihar.

Haka kuma gudumar ta fado kan Shugaban Hukumar Alhazai, Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan, wanda Alhaji Yusuf Lawan ya maye gurbinsa.

See also  Rejoinder: Disquiet In The Ministry Of marine and Blue Economy As Oyetola's Son Extortion Unsettles Workers

Labarai masu alaka
  Ku yi min addu’a, ba tattaki ba, Gwamnan Kano ya bukaci magoya bayansa
  IPAC ta yi Allah wadai da ADP kan sauya dan takarar gwamnan Kano
Wata fitacciyar ma’aikaciyar hukumar da korar ta shafa ita ce ‘yar marigayi Malamin addinin Musulunci, Sheikh Jafar Mahmud Adam, Malama Nana Aisha.

Sabbin mambobin kwamitin sun hada da Sheikh Abbas Abubakar Daneji, Sheikh Shehi Shehi Maihula, Munir Lawan, Sheikh Isma’il Mangu, Hajia Aishatu Munir Matawalle, da Dr Sani Ashir.

Sanarwar ta ce, ana sa ran wadanda aka nada za su karbi ragamar tafiyar da harkokin hukumar nan take, ta yadda za a samu nasarar gudanar da aikin Hajji a shekarar 2023.

Visited 1 times, 1 visit(s) today
Share Now